Kungiyar IPMAN Tace Mambobin Ta Ba Sa Iya Siyan Lita Dubu 45

Kungiyar dillalan man fetur ta kasa IPMAN ta koka kan yadda tace mafiya yawa daga cikin ‘ya’yan kungiyar ba sa iya siyan lita dubu 45, sakamakon tashin gwauron zabi da farashin man yayi, tun bayan janye tallafin da gwamnatin tarayya tayi.

Da yake ganawa da manema labarai, daya daga cikin manyan jiga jigai kuma tsohon shugaban kungiyar reshen jihar Ogun, Surajudeen Bada, yace a yanzu haka masu dillancin na man fetur sai sun hada kudi a tsakanin su suke iya siyan lita dubu 45, sannan su raba shi a tsakanin su.

Surajuddeen ya kuma alakanta wannan kalubale da cire tallafin man da gwamnatin Shugaba Tinubu tayi tun farkon hawan ta mulkin Najeriya, inda yace adadin man da suke siya a da kan farashin Naira miliyan 9, a yanzu naira miliyan 27 suke siyan sa.

Kazalika yace wasu daga cikin tsare tsaren da gwamnatin take bullo da su suna kawo cikas ga ‘yan kasuwa ta fannoni daban daban.

Leave a Reply