Kungiyar Inuwar Masarautar Bichi Ta Bukaci A Yi Watsi Da Batun Rushe Masarautun Jihar Kano

Wata kungiya mai suna Inuwar Masarautar Bichi ta bayyana rashin goyon bayan ta ga wata bukata da aka aikewa majalisar dokoki ta jihar Kano, wacce ke neman a samar da dokar da zata rushe masarautun jihar guda hudu.

Kungiyar Inuwar masarautar Bichi ta bayyana wannan matsayar tata ne a cikin wata wasika da ita ma ta aikawa majalisar dokokin, tana mai bayyana cewa rushe masarautun ka iya jawo matsaloli da suka hada da rashin zaman lafiya da kwanciyar hankali a tsakanin al’ummar jihar Kano, kamar yadda sakataren kungiyar Bello Gambo Bichi ya shaidawa manema labarai.

Kungiyar ta kuma ce tun bayan samar da masarautun an samu cigaba ta fannoni da dama musamman ma a masarautar Bichi, tana mai bada misali da cewa ko a zamanin baya lokacin kakanni an samu rabuwar masarautu wanda kuma hakan bai haifar da wata matsala ba.

Kazalika tace rushe masarautun zai kasance tamkar koma baya ne ga aikin majalisa, kasancewar a cikin ta ne aka sahale dokar kirkirar su, tana mai kira da a sake yin duba na tsanaki a kan batun.

Wannan dai na matsayin martani ga bukatar da wata kungiya mai sunan ‘Yan Dangwale ta aike wa majalisar, na neman a soke masarautun tare da dawo da tsohon sarki Muhammadu Sunusi na II.

Leave a Reply