Haka kuma karo na biyu da ta koma buga Europa League daga Champions League, bayan kakar 2000-2001, lokacin da ta yi ta uku bayan AC Milan da kuma Leeds United).

Barcelona tana ta bakwai a teburin La Liga da tazarar maki 16 tsakaninta da Real Madrid wadda take ta daya a babbar gasar Sifaniya.

Wannan ba matsayi ne mai kyau ba, domin tana son sake buga gasar Zakarun Turai a badi musamman Champions League, saboda haka sai ta kara sa kwazo a wasanninta, idan ba haka ba a badi ba za ta je gasar ba.

Kwallo biyu kacal Barcelona ta zura a raga a wasa shidan da ta yi a cikin rukuni a Champions League, gasar da ta ci mafi karancin kwallaye kenan.

Haka kuma kwallaye taran da aka zura mata a raga a bana, karo na biyu kenan da aka ci ta da yawa, bayan kakar 1997-98 da guda 14 suka shiga ragarta.

Kocin Barceloan Xavi ya zama na biyu da ya kasa cin wasa biyu a jere da fara karbar aiki, wanda ya yi canjaras daya da rashin nasara daya, bayan Luis Van Gaal da ya yi wannan rashin bajintar a 1997 da yin rashin nasara daya da shan kashi a wasa daya.

Barcelona na fatan komawa kan wasanninta a kakar nan, bayan da kungiyar ta ci karo da matsin tattalin arzikida da ya hada da bullar cutar korona.