Ku nemi makamai don kare kanku daga hare-haren ‘yan bindiga – Gwamnan Bauchi

Gwamnan jihar Bauchi da ke arewa maso yammacin Najeriya Bala Mohammed ya umarci al’umomin yankunan da aka kai wa hari a baya-bayan nan a yankin ƙaramar hukumar Alkaleri da su tashi tsaye, su nemi makamai domin su kare kansu daga farmakin ‘yan bindiga.

Jaridar Daily Trust a Najeriya ta ambato gwamnan na faɗin haka a fadar hakimin Yelwan Duguri a lokacin da ya ziyarci ƙauyukan Rimi da Gwana da Yalwan Duguri domin jajanta musu game da hare-haren ‘yan bindiga.

Dagacin garin Yelwan Duguri, Alhaji Adamu Mohammed Duguri ya ce mutum 20 ne suka mutu a ƙauyen Rimi lokacin da ‘yan bindigar suka kai hari garin.

Gwaman ya ce lamarin abu ne da ‘ba za a lamunta ba’ dan haka dole ayi duk abin da ya kamata, domin hana faruwar hakan a nan gaba.

”An san ku da jarunta, bai kamata ku bar mutanen nan su ci gaba da cutar da ku ba, dan haka ku kare garinku domin ƙwatar kawunanku, ya kamata ku tashi tseye, ku nemi makamai domin kare kanku”, in ji gwamnan.

Haka kuma ya shawarci mutanen da su zaƙulo ɓata-gari a cikin mutanen da ke haɗa kai da ‘yan bindiga, musamman waɗanda suke bai wa ‘yan bindigar bayanan sirri kan mutanen gari, yana mai cewa dole sai da ɗan gari akan ci gari.

Wannan dai ba shi ne karo na farko da wani gwamna a Najeriya ke umartar al’umma da su nemi makamai domin kare kansu ba.

Domin kuwa a shekarar 2021 ma gwamnan jihar Katsina da ke arewa maso yammacin ƙasar Aminu Bello Masari ya umarci al’ummar jiharsa da su nemi makamai domin kare kansu daga hare-haren ‘yan bindiga.

Leave a Reply