Kotun tarayya ta umarci hukumar EFCC da ta gabatar da A.A Zaura, a gabanta.
Kotun tarayya dake zamanta anan Kano ta umarci hukumar EFCC da ta gabatar da Abdussalam Abdulkareem da aka fi sani da A.A Zaura, kuma dan takarar Sanatan kano ta tsakiya a Jam’iyyar APC, gabanta domin amsa tuhumar da ake masa kan zamba cikin aminci da damfara.
A yayin zaman kotun a yau alhamis; Alkalin kotun Maishari’a Muhammad Nasiru Yunusa, ya bayyana cewa wanda ake tuhuma bai bayyana a gaban kotun ba! kamar yadda ya kauracewa zaman kotun guda biyu da aka yi a baya.
Ana dai zargin A.A Zaura da damfarar wani dan kasuwar Kuwait dala milyan dubu daya da milyan dari uku, biyo bayan wanke shi da kotun daukaka kara ta yi tun da fari, kotun na tarayya ta dawo da shari’ar domin yiwa kowanne bangare adalci.
Lauyan wanda ake kara Ibrahim Waru, ya ce an dage karar sakamakon rashin halartar wanda ake tuhuma, inda a gefe guda lauyan masu shigar da kara Abdulkareem Arogha, ya ce babu zancen ci gaba da shari’ar kasancewar wanda ake kara bai bayyana a gaban kotu ba.