Kotun ma’aikata dake zamanta a birnin tarayya Abuja, ta sanya ranar juma’a mai zuwa domin cigaba da sauraron kara tsakanin kungiyar likitoci masu neman kwarewa da gwamnatin tarayya dangane da turka turkar dake tsakanin su.
Mai shari’a Bashar Alkali ya umarci duka bangarorin biyu das u koma teburin sulhu domin tattaunawa kan matsalar da ke tsakanin su, wanda ta faro tun ranar 2 ga watan Agusta, wanda ya sanya kungiyar kilitocin ta tsunduma yajin aiki.
Kazalika a ranar juma’ar mai zuwa ne kuma mai shari’a Bashar zai karbi rahoton da aka samu bayan tattaunwar sasanci da bangaren gwamnatin tarayya tayi da kungiyar likitocin.
Tuni dai al’umma suke cike da fatan ganin an samu masalaha a tsakanin bangarorin biyu, duba da yadda marasa lafiya marasa adadi suka shiga wani hali sakamakon yajin aikin da likitoci masu neman kwarewa suka shiga.