Kotun Koli Zata Yanke Hukunci Kan Zaben Shugaban Najeriya ranar 26 Ga Watan Oktoba

Kotun Koli ta Najeriya zata yanke hukunci a ranar Alhamis kan jayayyar da ake yi na cancantar zaben da aka yiwa shugaba Tinubu a watan Fabrairu, kamar yadda kotun ta sanar a ranar Laraba, bayan da masu hammaya suka kalubalanci sakamakon zaben kan zargin rashin bin ka’ida wajen sanar da shi.

Atiku Abubakar na Jam’iyyar PDP da Peter Obi na jam’iyyar Labour, wadanda suka zo na biyu da na uku a zaben a kuri’un da aka kada, sun roki kotun a ranar litinin da ta soke hukuncin da kotun sauraron kararrakin zabe ta yanke, wanda ya tabbatar da nasarar Tinubu a wani yunkuri na karshe na juyar da sakamakon zaben zuwa ga wanda ya lashe zaben da kasashe da dama suka nuna gamsuwarsu da shi.

A ranar Litinin din da ta gabata ne dai jam’iyyun PDP da LP suka gabatar da ƙararrakinsu a gaban kotun, yayin da aka kori ƙarar da jam’iyyar APM da ɗan takarar ta na shugaban kasa, Chichi Ojei suka shigar bayan sun janye ta.

A ranar 6 ga watan Satumba ne kotun sauraron ƙararrakin zaben shugaban ƙasa ta yi watsi da ƙarar da bangarorin biyu suka shigar kan rashin isassun shaidu, amma Obi da Atiku sun ɗaukaka ƙara.

Hukuncin da kotun kolin za ta yanke a gobe dai shi ne na karshe.

Leave a Reply