Kotun koli ta ce Sadiq Wali ne dan takarar gwamnan Kano a PDP

Kotun Ƙolin Nijeriya ta kori ƙarar da Mohammed Abacha ya ɗaukaka gabanta, inda ta tabbatar Saddiq Wali a matsayin ɗan takarar gwamnan Kano na jam’iyyar PDP.

A cikin watan jiya ne, Kotun Ɗaukaka Ƙara a Kano ta jingine wani hukuncin Babbar Kotu, inda ta ce ba Mohammed Abacha ne ɗan takarar PDP ba, abin da ya sanya shi ɗaukaka shari’a zuwa Kotun Ƙoli.

Wanna na zuwa ne kwanaki 9 gabannin zaben gwamnoni a Najeriya, wanda dukkan mutanen biyu suke neman kujerar gwamnatin Kano karkashin jam’iyyar PDP.

Dr Yusuf Bello Dambatta shi ne mataimakin Sadiq Wali, ya shaidawa BBC hukuncin ya zo a daidai lokacin da suke bukatar hakan, ya ce abokin takarar su da suka je kotu tare Muhammad Abacha shi ya fara zuwa kotun farko ta kuma bashi dama, amma ba su karaya ba su ka sake garzayawa kotu ta biyu wato ta daukaka kara inda akai watsi da waccan shari’a da Alkali Liman ya yanke.

”Muhammad Abacha bai gamsu da hukuncin da kotun daukaka kara ta yi ba, shi ne ya sake garzayawa kotun koli, kuma cikin hukuncin Allah kotun ta yi watsi da kararrakin da aka shigar gabanta.

Daya ta Muhammad Abacha, dayar kuma ta hukumar zabe mai zaman kan ta wato INEC, da wadda shugaban jam’iyyar PDP Shehu Wada Sagagi ya shigar. Kotun ta tabbatar da Sadiq Wali a matsayin halattaccen dan takarar gwamna a jihar Kano karkashin inuwar jam’iyyar PDP,” in ji Danbatta.

Tun da fari babbar Kotun Tarayya a jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta yanke hukuncin cewa Muhammad Abacha ne ɗan takarar gwamnan jihar a ƙarƙashin jam’iyyar PDP.

Ya ce bangaren da suka gudanar da zaben fitar da gwani a Lugard Road shi ne halastaccen zaben dan takarar gwamnan na jam’iyyar PDP, kasancewar jami’an hukumar INEC sun halarci wurin tare da sanya ido kan zaben.

Wannan na zuwa ne kasa da kwanaki 10 a gudanar da zaben gwamnoni a Najeriyar, kawo yanzu babu wani martani da bangaren Muhammad Abacha ba su ce uffan kan wannan hukunci na kotun Kolin Najeriya ba.

Leave a Reply