Kotun Faransa ta yanke hukuncin daurin rai-da-rai kan Kunti Kamara na Liberia.

Wata Kotu a Faransa ta yanke hukuncin daurin rai-da-rai a kan Kunti Kamara, tsohon madugun ‘yan tawayen Liberia, bayan samun sa da aikata laifuka a lokacin da kasar ta yi fama da yakin basasa.

Shi dai Kunti Kamara, mai shekaru 47 a duniya, kotun wanda ta share kusan makwanni 3 ta na yi ma sa shari’a a birnin Paris, ta tabbatar da zarge-zargen aikata laifukan yaki, cin zarafin bil’adama da tozarta yaya mata da ake yi masa.

Wasu daga cikin shaidu da masu shigar da kara suka gabatar wa kotun sun hada da rawar da tsohon madugun ‘yan tawayen ya taka domin kashe wani malamin makaranta, wanda bayan an kashe shi, aka ciro masa zuciyarsa a bainar jama’a.

Har ila yau an gabatar da wasu shaidu da ke tabbatar da cewa Kamara ya jogaranci mayakan da suka aikata fyade sau da dama tsakanin shekarun 1993 zuwa 1994 lokacin da Liberia ke tsakiyar yakin basasa.

Kuntin Kamara dai ya kasance jigo a kungiyar Ulimo, daya daga cikin kungiyoyin da suka mamaye yankin arewa maso yammacin Liberia, kuma bayan wannan hukunci, alkalan kotu ya ba shi wanaki 10 domin daukaka kara idan ya na bukata.

Leave a Reply