Kotun Ƙoli Ta Tabbatar Da Nasarar Gwamna Abba Kabir Yusuf Na Jihar Kano

Kotun kolin Najeriya da ke zaman ta a Abuja ta tabbatar da nasarar da gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf na Jam’iyyar NNPP ya samu a zaɓen gwamna na shekarar 2023.

A hukuncin da ta zartar a yau Juma’a, kotun ta yi watsi da hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke, wanda ya ayyana Dakta Nasiru Yusuf Gawuna na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben.

Mai shari’a John Okoro wanda ya karanta hukuncin, ya ce kotun ɗaukaka ƙara ta yi kuskure wajen tabbatar da hukuncin kotun sauraron ƙorafin zaɓen jihar, wadda ta ce Abba Kabir bai samu rinjayen ƙuri’u a zaɓen ba.

A game da batun rashin kasancewar Abba Kabir ɗan jam’iyyar NNPP kuwa, kotun ta ce jam’iyya ce kawai take da ikon tantance wanda ɗanta ne ko kuma akasin haka.

Wannan dai shi ne mataki na ƙarshe a shari’ar da ake yi ta tantance ingancin nasarar da gwamnan ya samu a zaɓen na watan Maris.

Kazalika a zaman na ta na yau dai, kotun ta tabbatar da nasarar gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad da kuma takwaransa na jihar Legas Babajide Sanwo Olu, har ma Dauda Lawal na jihar Zamfara.

Leave a Reply