Kotu ta yi watsi da buƙatar Abba Kyari

Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yi watsi da buƙatar da tsohon shugaban sashen tattara bayanan sirri na rundunar ‘yan sandan Najeriya Abba Kyari ya gabatar a gabanta, yana neman kotun ta yi watsi da zarge-zargen da ake yi masa.

Yayin zaman kotuna a ranar Laraba alƙalin kotun mai shari’a Emeka Nwite ya yi watsi da buƙatar Abba Kyari, yana mai cewa kotun na da hurumin sauraron ƙararrakin da suke da alaƙa da ta’ammali da miyagun ƙwayoyi kamar yadda kundin tsarin mulki da dokar da ta kafa hukumar NDLEA suka ba ta dama.

Abba Kyari ya faɗa wa kotun cewa hukumar NDLEA ta yi gaggawar gabatar da shi a gaban kotu, tun kafin a kammala bincike, yana mai cewa kamata ya yi hukumar ta bai wa ‘yan sanda damar gudanar da binciken cikin gida, kafin ita NDLEA ta ɗauki mataki.

Ya ƙara da cewa ‘yan sanda sun gudanar da bincike kan lamarin kuma har sun gabatar da rahoton cikin gida ga rundunar ‘yan sanda.

Jami’in ‘yan sanda ya ce za a gabatar da shi a gaban kotu ne kaɗai, idan ‘yan sanda suka kammala gudanar da bincike.

Ya kuma ce dokar aikin ‘yan sanda ta ce hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda ta ƙasar na da ikon da za ta gudanar da bincike tare da ladabtar da jami’an ‘yan sanda, kamar yadda majalisar ƙoli ta ayyukan shari’a ke da ikon ladabtar da ma’aikatan shari’a.

To sai dai alƙalin kotun ya ce ikon da hukumar kula da ayyukan ‘yan sandan ke da shi , bai zarta ikon da kotun tarayyar ke da shi ba.

Kyari mai muƙamin mataimakin kwamshinan ‘yan sanda, tare da wasu mutum huɗu da ke aiki a rundana ɗaya na fuskantar tuhume-tuhumen haɗin baki wajen safarar hodar ibilis da nauyinta ya kai kilogiram 17.55

Leave a Reply