Kotu ta yanke wa Sufeto Janar na Najeriya hukuncin zaman gidan yari na watanni uku

Babbar Kotun Tarayyar Najeriya ta yanke wa Sufeton Ƴan sandan ƙasar hukuncin zaman gidan yari na wata uku.

Mai Shari’a Justice Mobolaji Olajuwon ce ta yanke hukuncin ga Usman Alkali Baba inda ta ce ya saɓa umarnin kotu kamar yadda kafar watsa labarai ta Channels a Najeriya ta ruwaito.

Tun farko dai wani ɗan sanda mai suna Patrick Okoli ne ya shigar da ƙara inda ya ce an yi masa ritaya ƙarfi da yaji a 1992 inda daga baya kotu ta bayar da umarnin a mayar da shi kan aikinsa tare da biyansa duka haƙƙoƙinsa.

Bayan nan hukumar kula da aikin ƴan sanda ta rubuta takarda mai kwanan wata 13 ga watan Oktoban 2004 ga babban sufeto na lokacin kan cewa a mayar da ɗan sandan kan muƙaminsa.

Haka ma a 2011 Mista Patrick ya ƙara shigar da wata ƙara domin a aiwatar da umarnin da kotu ta bayar tun farko na a mayar da shi kan aiki inda kotun kuma ta sake goyon bayansa.

Sai dai ofishin sufeto janar na lokacin ya ɗaukaka ƙara kan hukuncin.

Daga baya wanda yake ƙaran ya ƙara gaba har Majalisar Wakilan Najeriya inda su ma suka rubuta wa sufeton takarda.

Leave a Reply