Kotu ta rushe zaben fidda gwanin jam iyyar Apc na wasu yan majalisun jihohi 2 a jihar Yobe.

Babbar Kotun Taraiya dake da mazauni a Damaturu babban birnin jihar Yobe, ta jingine zabukan cikin gida biyu na ‘yan majalisar dokokin jihar na jam iyyar APC.

Da take yanke hukunci mai shari’a Fadima Aminu, ta umarci  jam’iyyar ta APC da ta sake shirya sabon zaben fidda gwanin cikin kwanaki 14 a mukaman da lamarin ya shafa.

Mazabun da hukuncin ya shafa sune Fika/Ngalfa da kuma Jaskusko.

Leave a Reply