Kotu Ta Dage Haramcin Kungiyar IPOB Tare Da Bada Umarnin Biyan Jagoran Ta Diyya
Alkalin babbar kotun Jihar Enugu, mai shari’a A. O. Onovo, ya ce ayyana kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biafra wato IPOB a matsayin haramtatciyar kungiya, ya sabawa kundin tsarin mulkin Najeriya.

Idan dai ba a manta ba, a shekarar 2017 ne kungiyar gwamnonin yankin kudu masu gabashin kasar karkashin jagorancin David Umahi, ta haramta ayyukan kungiyar, kafin daga bisani gwamnatin tarayya ta bayyana kungiyar a matsayin ta ta’addanci.
Sai dai jagoran kungiyar Nnamdi Kanu, ta hannun lauyansa Aloy Ejimakor, sun garzaya kotu don kalubalantar matakin.
Daga cikin bukatun kungiyar a gaban kotu, akwai bukatar ganin an sako jagoransu da warware wancan suna da aka sanya mata, sannan kuma suka nemi a baiwa Kanu diyar naira biliyan 8 na bata masa suna, da kuma tauye masa hakkinsa a matsayin sa na dan kasa.
A hukuncin da mai shari’a Onovo yayi, ya amince da dukkanin bukatun kungiyar ta IPOB, sannan kuma ya bukaci a baiwa Kanu hakuri ta hanyar wallafawa a jaridun kasar.