Kotu ta bayar da umurnin kama babban hafsan sojin kasa na Najeriya

Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Minna babban birnin, jihar Neja, ta bayar da umurnin kama babban hafsan sojin kasa na Najeriya, Janar Faruk Yahaya bisa laifin rashin grimama umarnin kotu.

Mai shari’a Halima Abdulmalik, wadda ta yanke hukuncin ta kuma bukaci da a kulle Janar Yahaya a gidan gyara hali na Minna saboda saba wa wani umurnin kotu na ranar 12 ga watan Oktoba, 2022.

Idan dai za’a iya tunawa a baya bayan nan ne itama wata babbar kotun da ke zaman ta a Abuja ta yanke wa sifeta-janar na ’yan sandan Najeriya Usman Baba Alkali hukuncin dauri na watanni uku saboda kin martaba hukuncin kotu.

Wannan umurni na zuwa ne bayan makamancinsa da wata kotu ta daban ta bayar a Abuja akan shugaban Hukumar EFCC Abdurasheed Bawa, saboda kin mutunta umurnin kotu. 

Wadannan hukunce hukunce sun haifar da mahawara a Najeriya, ganin irin mutanen da abin ya shafa da kuma batun mutunta umurnin kotu a lokacin mulkin dimokiradiya. 

Leave a Reply