Kotu Ta Ba Da Belin Tsohon Ministan Jiragen Saman Najeriya Hadi Sirika

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bayar da belin tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama Hadi Sirika, wanda ake zargi da karkatar da sama da Naira biliyan 2 daga asusun gwamnati.

Hukumar Yaki da Masu Karya Arzikin Kasa ta EFCC ta gurfanar da Hadi Sirika tare da ’yar sa Fatimah da wasu biyu ne kan badakalar kwangilar Naira biliyan 2 da miliyan dari 7 da aka bankado a ma’aikatar sufurin jiragen sama karƙashin jagorancinsa.
Hadi Sirika ya gurfana ne a gaban kotun tare tare Fatima da Jalal Hamma da kuma Kamfanin Al-Duraq Investment Ltd, a gaban Mai Shari’a Sylvanus Oriji na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja.
Hukumar EFCC na tuhumar su ne da laifin yin amfani da mukamansu wajen karkatar da kudaden daga ma’aikatar sufurin jiragan sama a zamanin shugabancin Hadi.
Sai dai bayan musanta tuhumar da ake musu ne, alkalin kotun ya bayar da belin su kan sharadin biyan naira miliyan 100 a kan kowannen su.

Leave a Reply