Kotu a Senegal ta wanke jagoran adawa Ousman Sanko daga zargin aikata fyade

Kotu a Senegal ta wanke jagoran adawa Ousman Sanko daga zargin aikata fyade a kan wata mata da ma zargin yi mata barazana da kalaman kisa, sai dai kotun ta tura shi gidan yari na shekaru 2 bisa laifin ingiza matasa

Sanko mai shekaru 48 wanda ya kara da Shugaba Macky salla zaben da ya gabata na shirin sake kalubalantarshi a zaben shekara mai zuwa, ya musanta duk wadannan laifi da kotu ta same shi da su.

Tun kafin wannan hukunci na yau Alhamis, jagoran adawa ya ce ba komai bane illa bita da kullin siyasa da wannan gwamnatin take mishi da ma kokarin ganin an hana shi tsayawa takara a zaben da ke tafe.

Tuni matakin na kotu ya janyo zanga-zabga daga bangaren magoya bayan madugun adawa.

Leave a Reply