Kocin tawagar kwallon kafa ta kasar Belgium, Roberto Martinez, ya bayyana rahotannin da ke danganta shi da karbar aikin horas da kungiyar Barcelona a matsayin jita-jita.
Kalaman na Marteniz sun zo ne sa’o’i bayan kin amsa tambayoyin da kocin Barcelona Ronald Koeman yayi a wani taron manema labarai a ranar Laraba.
Yanzu haka dai Koeman yana fuskantar matsin lamba a Camp Nou sakamakon rashin tabuka abin kirkin Barcelona a sabuwar kakar wasannin da aka shiga, musamman ma bayan kashin da ta sha a hannun Bayern Munich da 3-0 a gasar Zakarun Turai. Wannan ta sa a yanzu haka kocin kasar Belgium Roberto Martinez ya zama daga cikin wadanda ake alakantawa da maye gurbin mai horaswar na Barca.
Sai dai yayin wata ganawa da kafar labarin wasanni ta Eurosport, Martinez ya ce yada jita-jita ba sabon abu bane a fagen wasanni musamman na kwallon kafa, dan haka babu abin da zai ce kan rahotannin da ke yaduwa, domin kuwa babu wata alaka tsakaninsa da shirin horas da Barcelona.