Kocin Barcelona ya ja hankalin Dambele daya kara kwazo a kungiyar
Mai horas da ‘yan wasan Barcelona Xavi Hernandez, Yayi kira zuwa ga Ousmane Dembele akan ya cigaba da maida hankali a wasannin sa na gaba.
Xavi dai ya ajiye dan wasa Dembele a karawar da Barcelona tayi da Villareal a makon da ya gabata, Inda yayi amfani da Ansu Fati da Ferran Torres kuma sun taka rawar gani.
Duk da haka Xavi ya bayyana cewar Ousmane Dembele yana da matukar amfani a tawagar kungiyar sa.