Bayan da Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya fara gwada ƙwazon ministoci da sauran manyan muƙarrabban gwamnatinsa ƴan ƙasar da dama na zuba ido da sauraren abin da zai iya biyo baya.
A ranar Litinin ne 11 ga watan Oktoba 2021 Shugaban ya ƙaddamar da taron kwana biyu na karatun-ta-natsu wanda ministoci da manyan sakatarori da sauran manyan muƙarraban gwamnatin ke halarta domin bibiyar ayyukan gwamnatin a tsakiyar wa’adin mulkinsa na biyu.
Duk da cewa gwamnatin Shugaban a yayin buɗe taron ta ce ministocinta sun cimma kimanin kashi 60 cikin 100 na manufofi guda 9 da ta tsara ayyuka da shirye-shiryen da take aiwatar wa ‘yan ƙasar, akwai hasashen cewa wasu ministocin ka iya rasa muƙamansu bayan kammala taron a dalilin rashin bayar da gamsasshen sakamako na ayyukansu.
Idan dai ba a manta ba, a wata hira da BBC ta yi da kakakin Shugaba Buharin, Mallam Garba Shehu a watan Satumba, bayan cire Alhaji Sabo Nanono daga muƙamin ministan ayyukan gona da kuma Alhaji Saleh Mamman na ma’aikatar makamashi, kakakin ya ce matakin ”somin taɓi” ne.