Yanzu haka iyayen daliban sakandiren Tarayya ta Yawuri a jihar Kebbi da ‘yan bindiga suka sace na ci gaba da bayyana damuwa kan tsawon lokacin da ‘yayan nasu suka shafe a daji.
Ɗaliban dai yanzu haka sun shafe kimanin wata hudu bayan sace su, abin da ya sa iyayen yaran ke cewa sun yanke ƙauna da alwashin ceto ƴaƴan nasu da gwamnatin jihar Kebbi ta daɗe tana yi.
Wani mahaifi da ke cikin wadanda suka rasa ‘ya’yansu, ya shaida wa BBC cewa yanzu haka suna cikin matukar tashin hankali sakamakon rashin sanin halin da ‘ya’yan nasu ke ciki.
A cewarsa “Daga cikinmu ma wasu sun rasu, wasu sun hadu da rashin lafiya, mu kanmu Wallahi Tallahi da za a je a gwada mu sai an ga hawan jini ya kama mu, saboda halin da muke ciki na tashin hankali.”
Ya kara da cewa “Matan mu ne ma abin ya fi tayar musu da hankali, wani abin idan muna gaya muku sai ku ji kamar ma ba gaskiya muke fadi ba, kullum a ce yau a ce gobe, amma babu wani abu da muka gani a kasa har zuwa wannan lokaci”.
Shi ma wani daga cikin wadanda ‘ya’yansu ke hannun ‘yan bindigar ya bukaci gwamnati ta yi dukkan mai yiwuwa domin ganin an kubutar da yaran cikin ƙoshin lafiya.