Kabiru Adamu ya ce kusan watanni uku kenan tun daga watan Yuni ake samun irin wannan adadi, kamar yadda bincikensu ya gano.

Ya kuma kara da cewa matakan da wasu gwamnonin arewa maso yamacin kasar suka dauka wajen yaki da ‘yan bindiga sun ba wa gwamnatocin damar aiwatar da manufofinsu.

Sai dai akwai bukatar neman shawarwarin kungiyoyi irin nasu, don tabbatar da ikirarin da ake yi na cewa ana samun nasara a kansu.

“Dazuzzukan da ƴan bindigar nan ke bi sun ratsa jihohi da dama, don haka idan ba a dauki matakin bai daya, da kuma hada guiwa ga kasashe maƙwabta ba zai yi wuya a iya magance matsalar baki ɗaya” in ji shi.

Shugaban kamfanin nan Beacon Consulting ya ce rashin shigar da majalisun dokokin jihohin da aka sanya dokokin ya sa suna ganin cewa an yi wa Dimukradiyya karan tsaye.