KE DUNIYA: WANI MUMMUNAR HADARIN MOTOCI YA JIKKATA MUTANE DA DAMA A KANO.

Hadarin dai ya faru ne a kan titin Katsina dake nan Kano,a daidai lokacin da ake tsaka da shige da ficen fafutukar komawa gida, daga inda akazo domin samun abin kaiwa bakin salati wato kasuwa.
Tunda fari dai Direban Motar launin Lalloda mai daukar motoci a yayin da yake yo baya da motar da nufin shigar da motar ma ajiyarta, to saidai kan ya kai ga sarrafa kan motar tuni ya yi awon baya da wasu motoci biyu wadanda suke makare da mutane a cikinsu.
Kamar yadda wasu ganau suka bayyanawa filin ke Duniya cewa mutanen dake cikin motocin biyu sunkadu ainun, kan kuma daga cikinsu a kwai wadanda sukaji raunuka.
Baya ga dauke wadanda suka gamu da muggan raunuka zuwa Asibiti, Direban daya motar ya bayyana yadda suka tsinci kansu game da faruwar lamarin, inda ya ce suna cikin tafiya kawai suka tsinci kansu a cikin daya motar cikin mawuyacin hali.
A yanzu dai fatan wadancan bayin Allah shi ne musanman wadanda suka ji raunuka samun dauki da kulawa ta musanman ga kanfanin domin a yiwa kowanne bangare adalci.

Mustapha Abubakar Samammiya.

One thought on “KE DUNIYA: WANI MUMMUNAR HADARIN MOTOCI YA JIKKATA MUTANE DA DAMA A KANO.

  • November 16, 2022 at 5:29 pm
    Permalink

    Allah ya kiyaye, ya kare kara faruwar hakan nan gaba

    Reply

Leave a Reply