Kawu Sumaila ya doke Kabiru Gaya a zaɓen kujerar Sanatan Kano ta Kudu

Hon Kawu Sumaila na jam’iyyar NNPP ya samu nasarar lashe zaɓen kujerar Sanatan Kano ta Kudu a majalisar wakilai.

Da ake sanar da sakamon zaɓen a ofishin tatttara sakamakon zaɓen mazaɓar, INEC ta ce Kawu Sumaila ya yi nasara ne bayan samun kuri’u 319, 857.

Hukumar zaɓen ta ce ɗan takarar APC Kabiru Gaya, shi ne ya zo na biyu da kuri’u 192, 518, inda ɗan takarar PDP kuma ya zo na uku da kuri’u 14,880.

Leave a Reply