Karim Benzema ya zama na hudu a jerin wadanda ke kan gaba a cin kwallaye a Champions League.
Dan wasan tawagar Faransa shine ya ci wa Real Madrid kwallo a wasan Champions League da Sheriff ta yi nasara da ci 2-1 ranar Talata a Santiago Bernabeu.
Hakan ya zama na hudu a yawan cin kwallaye da 72 a raga, ya kuma hau kan Raul mai 71 a tarihin zazzaga kwallaye a Champions Leguea.
Cristiano Ronaldo ne kan gaba a cin kwallaye a gasar mai 135, sai Lionel Messi na biyu mai 121, wanda ya ci Manchester City a karawar da Paris St Germain ta yi nasara da ci 2-1 ranar Talata.