Karim Benzema ya zura kwallo tara a raga a La Liga yana gaban Haaland da Lwandowski da suka ci bakwai-bakwai kowanne a Bundesliga.
Dan kwallon tawagar Faransa ya sa kwazo a bana da ke kara fito da kansa kan zura kwallaye a raga tun da aka fara kakar bana.
Kawo yanzu ya ci kwallo tara, bayan buga wasannin mako na takwas a La Liga da hakan ya sa shine kan gaba a zura kwallo a raga a manyan gasar nahiyar Turai biyar.
Cikin gasar Ingila da Jamus da Italiya da kuma ta Faransa, ba dan wasan da ya ci kwallaye da yawa kamar Benzema.
Wadanda ke biye da shi sun hada da Haaland da kuma Lewandowski da kowanne ya ci bakwai-bakwai a Bundesliga.
Shi kuwa Salah da kuma Vardy kowanne ya zura kwallo shida-shida a raga a gasar Premier League;
A gasar Serie A, Immobile da Dzeko kowanne ya ci kwallo shida-shida haka ma Jonathan David da kuma Laborde da kowanne keda kwallo shida-shida a raga a gasar Ligue 1.