A ranar talata 5 ga watan afrilunan na shekara ta 2022 kungiyar kwallon kafa ta Benfica zata karbi bakunci kungiyar kwallon kafa ta Liverpool a gasar cin kofin zakarun nahiyar turai a wasan kusa dana kusa dana karshe.
Inda tuni mai horar da kungiyar ta Benfica Verissimo Nelson, yace ya karaya da wasan duba da cewa kungiyar tasa bata kai Liverpool karfi ba duba da irin zakakuran ‘yan wasan da take dasu kamar su; Salah, Mane, Faminoh, Silver sun fi ‘yan wasan kungiyar tasa kwarewa, amma yana mai karfafa musu gwiwar cewa suyi duk mai yiyuwa wajen ganin sun doke kungiyar ta Liverpool.
An dai kara sau goma tsakanin kungiyoyin biyu, inda Liverpool ta samu nasara sau 6, da kwallaye 19, yayin da ita kuma Benfica ta samu nasara sau 4 da kwallaye 11.