Karamar hukumar Nassarawa ta gina masallatai a wasu mazabun yankin

Anyi kira ga al ‘ummar karamar hukumar Nassarawa da su goyi bayan shugabancin karamar hukumar mai ci don samun nasarar abinda aka sanya a gaba.

Shugaban karamar hukumar Alhaji Auwalu Lawan Shu’aibu Aranposu yayi wannan kira lokacin da yake kewayen rangadi duba aikin masallatan da karamar a Mazabun Kaura Goje, Gama,Tudun wada, Dakata, Giginyu da kuma mazabar Gawuna a yankin karamar hukumar.

Yace majalisar karamar hukumar za ta yi duk mai yuwuwa wajen ganin ta cika muradun al’ummar ta.

Alhaji Auwalu Lawan Shu’aibu Aranposu yace duk da halin da tattalin arziqin kasar nan yake ciki, karamar hukumar zata cigaba da kokari wajen aiwatar da muhimman aiyukan da za su taimaki rayuwar al’ummar yankin kaitsaye.

Shima sakataren karamar hukumar   Alhaji Harazi Shu’aibu yayi kira ga wadanda za su ci gajiyar aikin suyi amfani da ta hanyoyin da suka kamata domin kaucewa fuskantar matsalar ambaliyar ruwa.

A jawabinsu daban daban shugaban majalisar kansilolin karamar hukumar Alhaji Musbahu Ahmed da shugaban sashin aiyuka na karamar hukumar,  Alhaji Shehu Sulaiman ya yabawa shugaban karamar hukumar bisa kokarin da yake samar da ingantattun aiyuka a karamar hukumar.

Leave a Reply