Kamfanin samar da man fetur na kasa NNPC ya kara yawan dilllansa
Kamfanin samar da man fetur na kasa NNPC ya kara yawan dilllansa daga 7 zuwa 20 a wani mataki na rage matsalar karancin man fetur da ake fama da shi a kasar nan.
Wannan matakin shi ne irin sa na farko a cikin shekaru 25 da suka gabata.
A cikin wata sanarwa da kamfanin ya fitar, ya bayyana cewa zai dinga siyarwa da dillalan nasa mai a farashin naira 148 kan kowacce lita.