Kamfanin Rarraba Hasken Lantarki Na KEDCO Ya Sha Alwashin Inganta Ayyukan Sa

Mukaddashin daraktan kamfanin rarraba hasken wutar lantarki na KEDCO Abubakar Yusuf, ya sha alwashin inganta ayyukan kamfanin domin tabbatar da cewa an cika wa al’umma muradun su.

Sanarwar da shugaban sashen sadarwa na kamfanin Sani Bala Sani ya fitar ga manema labarai, tace Abubakar Yusuf yayi wannan furucin ne yayin da ya kai ziyara ga daukacin ofisoshin kamfanin da ke jihohin Kano, Katsina da kuma Jigawa, domin tattaunawa da kuma bullo da tsaren tsaren inganta ayyukan su.

Yayin ziyarar tasa ya kuma gana da ma’aikatan kamfanin, inda ya bukaci hadin kai da goyon bayan su wajen ganin an cimma manufar gamsar da al’umma.

Ya kuma hore su da su kasance jakadu na gari, da kuma tabbatar da ganin duk wani koke da al’umma za su yi sun sanar wa da kamfanin domin daukar matakin da ya dace.

Leave a Reply