Kamfanin NNPCL Yayi Watsi Da Batun Karin Farashin Man Fetur A Najeriya

Kamfanin samar da man fetur na kasa NNPCL yace babu wani yunkuri daga bangaren sa na kara farashin mai a Najeriya.

Babban jami’in yada labarai na kamfanin Olufemi Soneye, shi ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya bukaci ‘yan Najeriya su yi watsi da jita jitar da ke cewa za a samu kari a farashin man.

A baya bayan nan dai ‘yan Najeriya sun shiga fargaba, sakamakon yadda ake samun rade radin da ke nuna yiwuwar tashin farashin man.

Sai dai kamfanin NNPCL ya bukaci al’umma su kwantar da hankalin su, kasancewar kamfanin yana daukar matakai domin ganin an rage kudaden da ake kashewa wajen shigo da man fetur din daga kasashen ketare.

Leave a Reply