Kamfanin NNPCL Yace Najeriya Za Ta Fara Fitar Da Tataccen Mai Kasar Waje A Shekarar 2024

Shugaban Kamfanin samar da mai na Najeriya Mele Kyari, ya ce kasar za ta fara fitar da tataccen man fetur da dangoginsa zuwa kasashen waje a shekarar 2024 mai kamawa.

Mele Kyari ya bayyana hakan ne lokacin da ya ziyarci shugabannin majalisar dattawa ta kasa.

Ya kuma bai wa ’yan Najeriya tabbacin cewa cikin watanni uku masu zuwa ba za a samu karancin man fetur ba, kamar yadda ake gani a lokacin bukukuwan Kirsimeti da Sabuwar Shekara, inda yace NNPC zai gyara matatar mai ta garin Fatakwal a wata mai kamawa, sannnan matatar mai ta Warri ta biyo baya a farkon shekarar 2024.

Da yake jawabi kan matsalar fasa bututu da satar mai, Kyari ya ce jami’an tsaro na musamman da ke yaki da bata-garin, sun taimaka musu wajen kwato gangunan danyen mai na kudade masu tarin yawa.

Da yake jawabi, shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya gode wa kamfanin man bisa hadin kai da ya bai wa Gwamnatin Tarayya wajen cire tallafin man fetur.

Leave a Reply