Kallo ya koma masarautar Rano kan shirin AGILE na bunkasa ilmin ‘ya’ya mata.

Shirin nan na Bunkasa Ilimin Yaya mata da tabbatar da walwalarsu na AGILE hadin Gwaiwa da bankin Duniya ya gudanar da wani taron masu ruwa da tsaki na  Kwana  Guda a karamar Hukumar Rano, domin bayyana hanyayin da shirin ya kusa musanman a fannin daya shafi ilimin yaya mata kaitsaye, kamar yadda Darakta a maaikatar Ilimi Aisha Inuwa Hussain, wadda kuma itace ta wakilci kwamishinan Ilimi na jihar Kano, ta bayyana cewa shirin zaifi maida hankali ne game da inganta tsarin tafiyar da ilimin yaya mata.

Shima a nasa jawabin Dr Auwal Halilu daga Jami ar Bayero, na daga cikin wadanda suka gabatar da mukala a gurin taron inda kuma mukalar tafi maida hankali kan matsalolin da ilimin yaya mata ke fuskanta.

Shugaban Shirin na AGILE Ado Tafida Zango ya ja hankalin Al`umma dasu zamo masu goyan bayan shirin domin cigaban yaya mata a ko  ina a fadin Jihar Kano.

A karshe Wakilimu Mustapha Abubakar Samammiya ya rawaito mana cewa Wakilan al`umma da malami da dalibai da dama ne suka sami halartar taron da aka gudanar a karamar Hukumar Rano.

Leave a Reply