Kalaman Minista Sun Jawo ‘Yan Majalisa Sun Bukaci Shugaban kasa Ya Tsige ta
Wakilan Neja-Delta a majalisar wakilan tarayya sun yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari da ya tsige Ministarsa, Sadiya Umar Farouq.
‘yan majalisar wakilan tarayyan sun nemi a tunbuke Sadiya Umar Farouq ne saboda kalaman da tayi a game da ambaliyar ruwa.
Kwanakin baya aka ji Ministar tana cewa jihar Jigawa ce jihar da ta fi kowace gamuwa da masifa a sakamakon ambaliyar da aka yi a daminar shekarar nan.
‘Yan majalisar sun yi wannan kira yayin da suka zanta da ‘yan jarida a Abuja. PT