‘Kalamaina na ‘ko da tsiya-tsiya’ ba na tunzura rikici ba ne’

Shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano, Abdullahi Abbas ya musanta zarge-zargen da ake masa na amfani da kalaman tunzura gangamin yaƙin neman zaɓe da tarukan siyasa.

Kalmar “ko da tsiya ko da tsiya-tsiya, sai sun ci zaɓe”, ba baƙon abu ne domin an sha jiyo Abdullahi Abbas na ambato wadannan kalamai a tarukan siyasa tun daga zaben 2019.

Ƴan adawa a jihar na cewa irin wadannan kalamai na Abdullahi Abbas, wata alama ce da ke nuna cewa mai yiwuwa akwai wani mummunan nufi da APC ta yi game da babban zaɓe da ke tafe a jihar.

Sai dai a tattaunawarsa da BBC, shugaban APCn a Kano ya ce an yi wa maganganunsa mummunar fahimta ce kawai.

Leave a Reply