KADDAMAR DA TARON BADA RIGAFIN KARIYA DAGA CUTAR SHAWARA. DA RABA MAGANI KYAUTA

Gwamnan Kano Dr Abdullahi umar ganduje, Ma’aikatar Lafiya ta kasa da Asusun tallafawa kasashen duniya, sun kaddamar da aikin rabon Gidan sauro mai dauke da magani da kuma Rijistar Sabuwar haihuwa kyauta a Faɗin Jihar nan.

Gwamna Ganduje wanda ya samu wakilcin Mataimakinsa Dr Nasiru Yusuf Gawuna ya jagoranci, kaddamar aikin rabon gidan sauron ne a Masarautar Gaya.

Da yake jawabi Ministan Lafiya Dr OSAGIE EHANIRE Wanda ya samu Wakilcin Babban Darakta a maikatar lafiya FESTUS OKOH Ya bayyana cewa jihar Kano tana daya dagacin jihohi Bakwai na kasar nan wadanda zasu amfana da gidan sauron wanda yawan sa ya haura Miliyan 8 Domin Rabawa al’ummar jihar kano.

Shima anasa jawabin Sarkin Gaya Dr Aliyu Umar ya mika godiya ta musamman ga gwamnatin kano kan kaddamar da shirin a masaurtar ta gaya, inda yaja hankalin Al’ummar da za su ci gajiyar gidan sauron da suyi amfani da shit a hanyoyin da suka kamata.

Anasa bangaren Mataimakin Gwamnan Kano Dr Nasiru Yusuf Gawuna ya ja hankalin iyaye Da su karbi wannan Rigakafin Domin kariya daga kamuwa da cutar shawara   Taron dai ya samu Halartar Kwamishinan lafiya Dr Aminu Ibrahim Tsanyawa, Shugaban maikatan fadar gwamnatin jihar kano, Shugaban Hisbah,UNICEF, WHO, Family Health,Da shauran Masu Ruwa da tsaki na harkar lafiya a fadin jihar nan.

Leave a Reply