Jirgin Virgin Atlantic yayi saukar gaggawa a Boston………

 Jirgin Virgin Atlantic yayi saukar gaggawa a Boston bayan da aka samu tashin wuta a jirgin.

Jirgin na kan hanyarsa ta zuwa landan daga birnin New York a ranar alhamis, inda wutar ta fara ci, hakan kuma ya sanya jirgin ya canja hanya domin ya sauka a birni mafi kusa dashi.

Babu wani wanda ya samu rauni kuma fasinjojin 217 sun samu kubuta ba tare da wata matsala a filin sauka da tashin jiragen sama na Logan ba.

Rundunar yan sanda ta ce wutar ta samo asali ne ta sanadiyar cazar waya.