Jerin yan wasan Real Madrid da za su buga wasan karshe a Copa del Rey da Osasuna

Real Madrid za ta kara da Osasuna a wasan karshe a Copa del Rey ranar Asabar a Estadio La Cartuja.

Real ta kai wannan matakin bayan da ta fitar da Barcelona, ita kuwa Osasuna ta yi nasara ne a kan Athleic Club.

Real Madrid mai Copa del Rey 19, za ta buga wasan karshe a gasar karo na 40, Osasuna wadda ba ta taba lashe Copa del Rey ba, za ta buga karawa ta biyu a wasan karshen.

Wannan shine karon farko da kungiyoyin za su fuskanci juna a fafatawar karshe a Copa del Rey.

Ranar 2 ga watan Octoban 2022 kungiyoyin sun tashi 1-1 Santiago Bernabeu a La Liga, amma Real ta ci 2-0 a gidan Osaasuna ranar 18 ga watan Fabrairu.

Real Madrid tana ta uku a teburin La Liga da maki 68, ita kuwa Osasuna mai maki 44 tana ta 10 a teburin babbar gasar tamaula ta Sifaniya ta bana.

Barcelona kan gaba a yawan lashe Copa del Rey mai 31, sai Athletic Bilbao mai 23, sannan Real Madrid mai guda 19 da kuma mai 10, Atletico Madrid.

Tuni Carlo Ancelotti ya sanar da ‘yan wasan da za su buga masa fafatawar.

‘Yan wasan Real Madrid:

Masu tsaron raga: Courtois, Lunin da kuma Luis López.

Masu tsaron baya: Carvajal, Militão, Alaba, Vallejo, Nacho, Odriozola, Lucas V., Rüdiger da kuma F. Mendy.

Masu buga tsakiya: Kroos, Modrić, Camavinga, Valverde, Tchouameni da kuma D. Ceballos.

Masu cin kwallaye: Hazard, Benzema, Asensio, Vini Jr., Rodrygo da kuma Mariano.

Leave a Reply