Jaruma Deepika Padukone ta kaddamar da ayyukan jinkai a Tamil Nadu

Bayan Jarumar ta dawo daga bikin nuna kawa da bajekolin kayan sawa a birnin Paris dake Kasar Faransa, ta zarce mahaifarta ta Tamil Nadu, dake kasar India, inda ta kaddamar da raba kayayyakin tallafi ga mutanen da ke fama da lalurar kwakwalwa.

Ta ce wannan ne aiki mafi girma da take alfahari da shi kamar yadda ta bayyana a shafukanta na sada zumunta.

Jarumai da kuma masoyanta da dama sun nuna farin cikinsu kan wannan tagomashi da Deepika Padukone, ta yiwa al’ummar Tamil Nadu.

Wani ya bayyana a shafinsa na twitter cewa ‘muna alfahari da ke’; wani ko cewa ya yi ‘lamarin sai sam-barka’ da dai sauransu.

 

Leave a Reply