Jam’iyyun adawa na kara kaimi wajen neman wanda zai kalubalanci Tinubu a 2027

Rahotanni na bayyana cewa ana samun ci gaba a tattaunawar da ake yi tsakanin Jagororin jam’iyyun hammaya na PDP da Labour Party don yin kama -kama wajen kawo ƙarshen gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027 da ke tafe.

A wata hira da aka yi da dan takarar jam’iyyar Labour, Peter Obi a baya baya nan ya ce ceto Najeriya daga halin da take ciki shi ne babban abinda yake fatan za su yi aiki tare domin ganin hakan ta tabbata, ba wai batun kashin kansa na zama shugaban Najeriya ba.

Obi ya kuma yabawa Atiku Abubakar bisa wasu kalamai da aka ruwaito ya yi a baya baya nan da ke nuna alamun amincewarsa kan tattaunawar domin hadin kai da zimmar tunkarar shugaba Tinubu na jam’iyyar APC mai Mulki a zaben 2027 da ke tafe.

Mai magana da yawun jam’iyyar ta Labour Dr Tanko Yunusa, ya shaida wa Manema Labarai cewa fatansu shi ne su hada kai domin su cimma nasara, inda yace a halin yanzu jiga-jigan jam’iyyun biyu na tattaunawa wajan neman wanda ya cancanta.

Leave a Reply