Jam’iyyar PDP mai adawa a Najeriya ta bukaci Gwamnan Babban Bankin kasar Godwin Emefiele da ya gaggauta sauka daga mukamin sa saboda abinda ta kirawa gazawa sakamakon yadda darajar kudin kasar na naira ke ci gaba da faduwa.
Jam’iyyar tace jagorancin Emefiele a bankin, a karkashin gwamnatin APC ya haifar da matukar koma baya dangane da fasalin kudin kasar wanda ya haifar da hauhawan farashin kayan masarufi dake shafar talaka.
Sakataren yada labaran Jam’iyyar Kola Ologbondiyan yace Emefiele ya karbi jagorancin bankin a shekarar 2014 lokacin da ake sayar da Dalar Amurka guda akan naira 164, amma ayau darajar naira yayi mummunar faduwar da ake sayen Dala guda akan naira 600.
Ologbondiyan yace Babban bankin ya gaza aiwatar da manufofin sa a karkashin Emefiele, inda ya mayar da hankalin sa wajen farfaganda da kuma aiwatar da manufofin dake illa ga talakawa, maimakon samo hanyoyin da zai saukaka musu rayuwar su.
Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya nada Emefiele a matsayin Gwamnan Babban Bankin a shekarar 2014, yayin da Buhari ya nada shi domin yin wa’adi na biyu bayan kammala wa’adin sa na farko na shekaru 5.