Jam’iyyar Labour Ta Karbi Tayin Da Atiku Abubakar Yayi Na Hade Kai Tsakanin Jam’iyyun Hamayya

Jam’iyyar Labour Party ta bayyana yin maraba da tayin da tsohon mataimakin shugaban Najeriya, kuma dan takarar shugaban kasa a zaben shekarar 2023 na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar yayi, na hade kai tsakanin jam’iyyun hamayya, da kuma kawo karshen wanzuwar jam’iyyar APC a mulki.

Atiku Abubakar dai yayi wannan tayi ne sakamakon abin da ya bayyana da cewa Najeriya na gabar fadawa kan tsarin jam’iyya daya, wanda yace hakan babu abin da zai haifar sai gurgunta tafiyar dimukradiyyar kasar.

A wata hira ta musamman da babban sakataren jam’iyyar ta Labour na kasa Obiora Ifoh yayi da wani gidan talabijin, ya bayyana cewa kiran na Atiku abu ne da ya kamata a ce kowane dan Najeriya yayi maraba da shi.

A gefe guda kuwa jam’iyyar NNPP tace akwai yiwuwar ta karbi wannan tayi, sai dai ta gindaya sharadin cewa har sai idan Atiku zai goyi bayan jagoran jam’iyyar wato Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso a zaben shekarar 2027 da ke tafe.

Leave a Reply