Jam’iyyar APC na dari-dari kan amfani da na’ura a lokacin zabe

Shugaban jam’iyyar APC na Kasa, Sanata Abdullahi Adamu ya nuna damuwa  a kan shirin da hukumar zaɓe ke yi na aiki da na’urar tantance masu zaɓe da aika sakamako ta intanet da ake kira BVAS a babban zaɓen da ke tafe.

Kalaman nasa na zuwa ne yayin da ya rage kwanaki 93 a gudanar da zaben  shugaban kasar Najeriya.

Shugaban Jam’iyyar ta APC  ya ce yana shakkar amfani da na’aurar ta BVAS zai samar da kyakkyawan sakamako ga al’ummar kasar baki daya a zaben 2023.

A cewarsa  Najeriya ba ta shirya amfani da wannan fasaha a lokacin zabe ba  amma kuma ya ce idan za a yi to ya zama wajibi ga hukumar zabe ta tabbatar wa ‘yan Najeriya ta shirya dari bisa dari don ta gamsar da kowa.

Sanata Abdullahi Adamu ya ce akwai ƙalubale sosai da ya shafi rashin wutar lantarki da rashin layukan intanet a yankunan karkara wanda idan ba a shawo kansa ba, zai yi wuya na’urar ta yi tasiri.

Leave a Reply