Hukumar gudanarwar jami’ar Adekunle Ajasin ta jihar Ondo, ta sanya dokar hana sanya matsatstsun kayan da basu kamata ba a jami’ar.
An yi tanadin dauar matakin dakatarwa a kan duk dalibin da aka samu da saba wannan doka.
Kamar yadda BBC ta wallafa a shafinta na yanar gizo tace, cikin wata sanarwa da aka raba wa daliban jami’ar mai dauke da kwanan watan 7 ga watan Satumban nan, jami’ar ta nuna damuwa kan yadda ta ce dalibai na yawan yin shigar da bata kamata ba a makaantar.
Sanarwar ta ce bayan zuzzurfan bincike, wannan makaranta ta yanke shawarra cewa daga yanzu za a dakatar da duk wanda aka samu da saba wannan ka’ida tsawon wata guda, farawa daga ranar 25 ga watan Agusta.