Jami’ar BUK ta musanta  batun komawa zangon karatu na 2022/2023

Hukumar gudanarwa ta Jami’ar Bayero kano, ta nesanta kanta daga wata takarda dake yawo a shafinka sada zamunta, mai dauke da tsarin zangon karatu na 2022/2023.

Bayanin hakan na dauke cikin wata sanarwa da jami’ar ta fitar ranar Talata, mai dauke da sa hannun mataimakin magatakardan Jami’ar mai kula da bangaren yada labarai da hulda da jama’a, Lamara Garba Azare.

Sanarwar ta kara da cewa hukumar jami’ar zata fitar da tsarin zagon karatun nan bada jimawa.

A karshe ya shawarci dalibai dasu kauracewa labaran marasa tushe wadanda zasu nemi su haifar musu da rudani a zukatansu.

Leave a Reply