Jami’an tsaron Najeriya sun kuɓutar da wata soja da ‘yan bindiga suka sace

Jami’an tsaro a Najeriya sun ce sun kuɓutar da wata soja da ‘yan bindiga suka sace ta a ranar Litinin da ta gabata.

Jaridar Punch a Najeriya ta ruwaito cewa ‘yan bindigar sun sace tare da yin garkuwa da sojar mai suna Lt. PP Johnson.

A wani faifan bidiyo da ‘yan bindigar suka fitar bayan sace sojar, an ga ɗaya daga cikin ‘yan bingigar na shan alwashin kai wa sojojin Najeriya hare-hare.

Ya kuma ce su ba ‘yan ƙungiyar IPOB ba ne, amma suna buƙatar ɓallewa daga ƙasar.

To sai dai a wata sanarwa da rundunar sojin ƙasar ta fitar ranar Alhamis ta ce an kama waɗanda suka sace sojar, bayan jami’an tsaron ƙasar sun kuɓutar da ita ranar Alhamsi da rana a wani daji da ke kan iyakar jihohin Enugu da Imo da ke kudu maso gabashin ƙasar.

Leave a Reply