Jakadan Faransa ya fice daga Jamhuriyar Nijar

Jakadan Faransa a Jamhuriyar Nijar, Sylvain Itté ya fice daga Yamai, babban birnin ƙasar ta Nijar da sanyin safiyar Laraba, kuma yanzu hakan ya tashi a jirgin sama daga birnin Ndjamena na ƙasar Chadi zuwa gida Faransa.

A watan da ya gabata ne ma’aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Nijar ta bai wa jakadan wa’adin kwana biyu ya fita daga ƙasar.

Nijar ta ɗeba wa ambasadan wa’adin ne bayan ya ƙi yarda ya gana da jagororin mulkin soji na ƙasar waɗanda suka hamɓarar da gwamnatin shugaba Mohamed Bazoum a watan Yuli.

Har yanzu sojojin na ci gaba da tsare Bazoum da iyalansa a fadar shugaban ƙasa.

Nijar dai na ɗaya daga cikin ƙasashen da Faransa ta yi wa mulkin mallaka, kuma har yanzu akwai sojojin Faransar 1,500 a ƙasar ta Nijar.

Shugaba Emmanuel Macron ya bayyana cewa dakarun Faransa za su fice daga Nijar ɗin kafin ƙarshen wanan shekara.

Leave a Reply