Iyalan ‘Yansanda 613 Da Suka Rasa Rayukansu Sun Samu Tallafin Sama Da Naira Biliyan 2

Iyalan jami’an ‘yansanda 613 da suka rasa rayukansu a bakin aiki sun samu tallafin sama da Naira biliyan 2, domin dogaro da kawunan su wajen tafiyar da harkokin rayuwa na yau da kullum.

Wannan tallafi dai ya zo ne karkashin wani tsarin taimako na hadin gwiwa daga gwamnatin tarayya da kuma rundunar ‘yan sanda ta Najeriya.

Da yake mika takardun chakin kudin ga iyalan mamatan a babban birnin tarayya Abuja, babban sufeton ‘yan sanda na kasa Kayode Egbetokun, ya ja hankalin su da suyi amfani da kudaden ta hanyoyin da suka dace.

Kazalika yace hakan wani yunkuri ne daga rundunar ‘yansanda ta kasa, domin tausayawa da kuma kyautatawa iyalan da mamatan ‘yansandan suka bari, kasancewar suna fuskantar tarin kalubale a lokuta da dama.

Leave a Reply