Israela zata gudanar da sabon zabe

  • Isra’ila zata gudanar da sabon zabe bayan shugaba Netanyahu ya gaza samar da gwamnatin hadaka.

Daukacin mambobin majalisar dokokin Kasar Isra’ila sun sha alwashin rusa zauren majalisar  bayan shugaba Natanyahu ya kasa cika ka’idar neman goyon bayan dukkannnin jam’iyyun Kasar wajen samar da gwamnatin Hadaka.

“yan majalisar sun tabbatar da cewa za’a sake gudanar da zaben majalisar dokokin Kasar da zai tabbatar da sobon firaimistan Isra’ila, a watan satumbar wannan shekara.

A watan Afrilu ne Benjamin Natanyahu, ya lashe zaben Kasar a karo na biyar bayan jam’iyyarsa ta Likud, ta samu kujeru 35 daga cikin 120 a zauren majalisar dokokin Kasar.

Natanyahu na fuskantar tuhume-tuhume uku bisa zargin cin hanci da rashawa, duk da yayi watsi da zarge-zargen, yace ‘yan adawa ne ke masa bita da kulli domin ganin bayansa.