INEC ta kayyade adadin gudummawar da za iya bawa ‘yan takara

Hukumar Zabe mai zaman kanta ta Kasa ta gargadi ’yan takara da ma jam’iyyu da kada su kuskura su karba ko su bayar da gudunmawar da ta wuce ta Naira miliyan 50 a babban zaben 2023 mai zuwa.

Gargadin na kunshe ne a cikin wani kundin ka’idojin shirya gangami, yakin neman zabe da samar da kudaden da ’yan takara za su kashe yayin zaben 2023, wanda hukumar ta fitar jiya juma’a a Abuja.

Kundin ya nuna abin da jam’iyya za ta kashe ya kunshi duk wasu kudade ko kayan aiki da jam’iyya ko dan takara zai kashe, kuma dole ne a wallafa su kafin ranar zabe.

Haka zalika, Kundin ya kuma ce kudaden da ake magana a kansu sun hada da na kararrakin da za a shigar a kotu, da na abubuwan da za su biyo bayan zabe da kararrakin bayan zabe da kuma na sake hada kan ‘yan jam’iyya bayan kammala zaben.

Leave a Reply